Pular para o conteúdo
Publicidade

Galatiyawa 6:1-5

Yin alheri ga kowa

1 ’Yan’uwa, in an kama wani yana cikin yin zunubi, ku da kuke masu ruhaniya ya kamata ku komo da shi a kan hanya a hankali. Amma ku lura da kanku, domin kada maimakon dawowa da ɗan’uwanku, ku ma ku fāɗi cikin jarraba. 2 Ku ɗauki nawayar juna, a haka kuwa za ku cika dokar Kiristi. 3 In wani yana tsammani shi wani abu ne alhali kuwa shi ba kome ba, ruɗin kansa yake yi. 4 Kowa yă auna ayyukansa. A sa’an nan ne zai iya yin taƙama da kansa, ba tare da kwatanta kansa da wani ba, 5 gama kowa zai ɗauki kayansa.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.