1 A dā Allah ya yi wa kakanni-kakanninmu magana ta bakin annabawa a lokuta dabam-dabam da kuma a hanyoyi iri-iri, 2 amma a waɗannan kwanaki a ƙarshe ya yi magana da mu ta wurin Ɗansa, wanda ya naɗa magājin dukan abubuwa, wanda kuma ta wurinsa ya halicci duniya.