12 Ku lura fa, ’yan’uwa, cewa kada waninku yă kasance da zuciya mai zunubi marar bangaskiya da takan juye daga bin Allah mai rai. 13 Sai dai ku ƙarfafa juna kullum, muddin akwai lokacin da ana ce da shi Yau, don kada waninku yă zama mai taurin zuciya ta wurin ruɗun zunubi.