Gargaɗi a kan rashin bangaskiya
7 Kamar dai yadda Ruhu Mai Tsarki ya ce,
"Yau, in kuka ji muryarsa,
8 kada ku taurare zukatanku,
yadda kuka yi a tawayen nan,
a lokacin gwaji a hamada,
12 Ku lura fa, ’yan’uwa, cewa kada waninku yă kasance da zuciya mai zunubi marar bangaskiya da takan juye daga bin Allah mai rai. 13 Sai dai ku ƙarfafa juna kullum, muddin akwai lokacin da ana ce da shi Yau, don kada waninku yă zama mai taurin zuciya ta wurin ruɗun zunubi. 15 Kamar yadda aka faɗa cewa,
"Yau, in kuka ji muryarsa,
kada ku taurare zukatanku
kamar yadda kuka yi a tawayen nan."3.15 Zab 95.7,8