Pular para o conteúdo
Publicidade

João 11

Mutuwar Lazarus

1 To, an yi wani mutum mai suna Lazarus wanda ya yi rashin lafiya. Shi daga Betani ne, ƙauyen su Maryamu da yar’uwarta Marta. 2 Maryamun nan kuwa, wadda ɗan’uwanta Lazarus yake rashin lafiya, ita ce ta zuba wa Ubangiji turare ta kuma goge ƙafafunsa da gashin kanta. 3 Saboda haka yan’uwansa mata suka aika da saƙo wa Yesu cewa, "Ubangiji, wannan da kake ƙauna yana rashin lafiya."

4 Sa’ad da ya ji haka, sai Yesu ya ce, "Wannan rashin lafiya ba zai kai ga mutuwa ba. A’a, sai dai don a ɗaukaka Allah a kuma ɗaukaka Ɗan Allah ta wurin wannan." 5 Yesu kuwa yana ƙaunar Marta da yar’uwarta da kuma Lazarus. 6 Duk da haka sa’ad da ya ji Lazarus ba shi da lafiya, sai ya ƙara kwana biyu a inda yake.

7 Sai ya ce wa almajiransa, "Mu koma Yahudiya."

8 Sai suka ce, "Rabbi, ba da daɗewa ba ne Yahudawa suka nemi su jajjefe ka, duk da haka za ka koma can?"

9 Yesu ya amsa ya ce, "Ba sa’a goma sha biyu ce yini guda ba? Mutumin da yake tafiya da rana ba zai yi tuntuɓe ba gama yana ganin hasken duniyan nan. 10 Sai a sa’ad da yake tafiya da dare ne zai yi tuntuɓe, don ba shi da haske."

11 Bayan ya faɗa haka, sai ya ƙara ce musu, "Abokinmu Lazarus ya yi barci, amma za ni in tashe shi."

12 Almajiransa suka ce, "Ubangiji, in barci ne yake, to, ai, zai sami sauƙi." 13 Yesu kuwa yana magana mutuwarsa ce, amma almajiransa suka ɗauka yana nufin barcin gaskiya ne.

14 Saboda haka sai ya gaya musu a fili cewa, "Lazarus ya mutu,

Veja também