13 Kuma zan yi duk abin da kuka roƙa cikin sunana, don Ɗan ya kawo ɗaukaka ga Uban. 14 Za ku iya roƙe ni kome a cikin sunana, zan kuwa yi.
Yesu ya yi alkawarin Ruhu Mai Tsarki
15 "In kuna ƙaunata za ku yi biyayya da umarnina. 16 Zan kuwa roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimakon da zai kasance tare da ku har abada,