Pular para o conteúdo
Publicidade

Yohanna 15

Itacen inabi da kuma rassa

1 "Ni ne kuringar inabi na gaskiya, Ubana kuwa shi ne manomin. 2 Yakan sare kowane reshe a cikina da ba ya ya’ya, amma yakan ƙundume kowane reshe da yake ba da ya’ya, domin ƙara ba da ya’ya. 3 Kun riga kun zama masu tsabta saboda maganar da na yi muku. 4 Ku kasance a cikina, ni kuma zan kasance a cikinku. Babu reshen da zai iya yin ya’ya da kansa, dole kasance a jikin kuringar inabin. Haka ku ma, ba za ku iya ba da ya’ya ba sai kun kasance a cikina.

5 "Ni ne kuringar inabin; ku ne kuma rassan. In mutum ya kasance a cikina ni kuma a cikinsa, zai ba da ya’ya da yawa; in ba tare da ni ba, ba za ku iya yin kome ba. 6 Duk wanda bai kasance a cikina ba, yana kamar reshen da aka jefar bushe; irin waɗannan rassan ne akan tattara, a jefa cikin wuta a ƙone. 7 In kun kasance a cikina kalmomina kuma suka kasance a cikinku, ku roƙi kome da kuke so, za a kuwa ba ku. 8 Wannan ne yakan kawo ɗaukaka ga Ubana, ku ba da ya’ya da yawa, kuna kuma nuna kanku ku almajiraina ne.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também