23 Da sojojin suka gicciye Yesu, sai suka ɗibi tufafinsa suka kasa kashi huɗu, kowanne ya ɗauki kashi ɗaya. Suka kuma ɗauki taguwarsa, taguwar kuwa ba ɗinki, saƙa ɗaya ce gudanta daga sama har ƙasa.
24 Sai suka ce wa juna, "Kada mu yage ta, sai dai mu jefa ƙuri’a a kanta mu ga wanda zai ci."
Wannan ya faru ne don a cika nassin da ya ce,
"Suka rarraba tufafina a junansu,
suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigata."19.24 Zab 22.18
Abin da sojojin suka yi ke nan.
25 To, tsaye kusa da gicciyen Yesu kuwa akwai mahaifiyarsa, tare da ’yar’uwar mahaifiyarsa, Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magdalin. 26 Sa’ad da Yesu ya ga mahaifiyarsa a can, da kuma almajirin nan da yake ƙauna tsaye kusa, sai ya ce wa mahaifiyarsa, "Mace, ga ɗanki," 27 ga almajirin kuwa ya ce, "Ga mahaifiyarka." Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa.