39 Yana tare da Nikodimus, wannan da ya taɓa zuwa wurin Yesu da dare. Nikodimus ya zo da mur da aloyes a gauraye, wajen awo ɗari. 40 Da ɗaukowar jikin Yesu, sai su biyun suka nannaɗe shi tare da kayan ƙanshi a cikin ƙyallayen lilin bisa ga al’adar Yahudawa ta jana’iza.