13 Da lokacin Bikin Ƙetarewa na Yahudawa ya yi kusa, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima. 14 A filin haikali ya sami mutane suna sayar da shanu, tumaki da tattabaru, waɗansu kuma zaune a tebur suna canjin kuɗi. 15 Saboda haka ya tuƙa bulala ta igiyoyi, ya kori duka daga filin haikali, har da tumaki da shanu; ya watsar da kuɗin masu canjin, ya birkice teburansu. 16 Ga masu sayar da tattabaru kuwa ya ce, "Ku kwashe waɗannan daga nan! Don me za ku mai da gidan Ubana kasuwa!" 17 Sai almajiransa suka tuna cewa a rubuce yake, "Himma saboda gidanka zai cinye ni."2.17 Zab 69.9
Publicidade