Yesu ya bayyana ga Maryamu Magdalin
11 Maryamu kuwa ta tsaya a bakin kabarin daga waje tana kuka. Da tana cikin kuka, sai ta sunkuya ta leƙa cikin kabarin, 12 sai ta ga waɗansu mala’iku biyu saye da fararen tufafi, zaune a inda dā gawar Yesu take, ɗaya wajen kai ɗayan kuma wajen ƙafafu.
13 Suka tambaye ta cewa, "Mace, don me kike kuka?"
Ta ce, "Sun ɗauke Ubangijina, ban kuma san inda suka ajiye shi ba." 14 Da ta faɗin haka, sai ta juya ta ga Yesu tsaye, sai dai ba tă gane cewa Yesu ne ba.
15 Sai ya ce, "Mace, don me kike kuka? Wa kike nema?"
Ta yi tsammani shi ne mai aikin lambun, sai ta ce, "Ranka yă daɗe, in kai ne ka ɗauke shi, gaya mini inda ka ajiye shi, in je in ɗauke shi."
16 Yesu ya ce mata, "Maryamu."
Sai ta juya wajensa ta ɗaga murya ta ce da Arameyanci, "Rabboni!" (Wanda yake nufin "Malam").
17 Yesu ya ce, "Kada ki riƙe ni, gama ban riga na koma wajen Uba tukuna ba. A maimako, ki tafi wajen ’yan’uwana ki gaya musu, ‘Ina komawa wajen Ubana da Ubanku, wajen Allahna da kuma Allahnku.’ "
18 Sai Maryamu Magdalin ta wajen almajiran da labari cewa, "Na ga Ubangiji!" Ta kuma gaya musu cewa ya faɗa mata waɗannan abubuwa.