Warkarwa a tafki
1 Bayan an ɗan jima, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima don wani bikin Yahudawa. 2 To, a Urushalima akwai wani tafki kusa da Ƙofar Tumaki, wanda a yaren Arameyik ake kira Betesda5.2 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da Betzata; waɗansu kuma suna da Betsaida ne a nan. an kuma kewaye shi da shirayi biyar. 3 A nan naƙasassu da yawa sukan kwanta, makafi, guragu, shanyayyu.5.3 Waɗansu rubuce-rubucen hannu marar muhimmanci sosai suna da shanyayyu, kuma suka jira a motsa ruwaye. 4 Lokaci-lokaci mala’ikan Ubangiji yakan sauko ya motsa ruwaye. Mutum na farko da ya shiga tafkin bayan motsawa zai warke daga kowace cutar da yake da ita. 5 Akwai wani da yake nan ba shi da amfani shekara talatin da takwas. 6 Da Yesu ya gan shi kwance a can ya kuma sami labari cewa ya daɗe a wannan hali, sai ya tambaye shi, "Kana so ka warke?"
7 Marar amfanin nan ya ce, "Ranka yă daɗe, ba ni da wanda zai taimaka yă sa ni a cikin tafkin sa’ad da aka motsa ruwan. Yayinda nake ƙoƙarin shiga, sai wani yă riga ni."
8 Sai Yesu ya ce masa, "Tashi! Ɗauki tabarmarka ka yi tafiya." 9 Nan take mutumin ya warke; ya ɗauki tabarmarsa ya yi tafiya.
A ranar da wannan ya faru ranar Asabbaci ce,