Yesu ya ciyar da dubu biyar
1 Ɗan lokaci bayan wannan, sai Yesu ya ƙetare zuwa gaɓar mai nesa na Tekun Galili (wato, Tekun Tibariya), 2 sai taro mai yawa na mutane suka bi shi domin sun ga abubuwan banmamakin da ya yi ga marasa lafiya. 3 Sa’an nan Yesu ya hau gefen dutse ya zauna tare da almajiransa. 4 Bikin Ƙetarewan Yahudawa ya yi kusa.
5 Sa’ad da Yesu ya ɗaga kai ya ga taro mai yawa suna zuwa wajensa, sai ya ce wa Filibus, "Ina za mu sayi burodi saboda mutanen nan su ci?" 6 Ya yi wannan tambayar don yă gwada shi ne kawai, gama ya riga ya san abin da zai yi.
7 Sai Filibus ya amsa ya ce, "Kai, ko albashin wata takwas ba zai iya sayan isashen burodin da kowa zai ɗan samu kaɗan ba!"
8 Sai wani daga cikin almajiransa Andarawus, ɗan’uwan Bitrus, ya yi magana, 9 "Ga wani yaro da ƙananan burodin sha’ir guda biyar da ƙananan kifi biyu, amma me wannan zai yi wa yawan mutanen nan."
10 Yesu ya ce, "Ku sa mutanen su zauna." Wurin kuwa akwai ciyawa da sosai, sai maza suka zazzauna, sun kai wajen dubu biyar. 11 Sa’an nan Yesu ya ɗauki burodin, ya yi godiya, ya kuma rarraba wa waɗanda suke zaune gwargwadon abin da ya ishe su. Haka kuma ya yi da kifin.
12 Sa’ad da duk suka ci suka ƙoshi, sai ya ce wa almajiransa, "Ku tattara gutsattsarin da suka rage. Kada kome yă lalace." 13 Saboda haka suka tattara su suka kuma cika kwanduna goma sha biyu na gutsattsarin burodin sha’ir biyar nan da suka ragu bayan kowa ya ci.
14 Bayan mutanen suka ga abin banmamakin da Yesu ya yi, sai suka fara cewa, "Lalle, wannan shi ne Annabin nan mai zuwa duniya."