66 Daga wannan lokaci da yawa daga cikin almajiransa suka ja da baya, suka daina bin sa.
67 Sai Yesu ya tambayi Sha Biyun, "Ku ma za ku tafi ne?"
68 Sai Siman Bitrus ya amsa ya ce, "Ubangiji wajen wa za mu tafi? Kai ne da kalmomin rai madawwami. 69 Mun gaskata mun kuma san cewa kai ne Mai Tsarkin nan na Allah."