Yesu ya koyar a bikin
14 Sai bayan da aka kai tsakiyar Bikin, sa’an nan Yesu ya haura zuwa filin haikali ya fara koyarwa. 15 Yahudawa suka yi mamaki suna tambaya, "Yaya wannan mutum ya sami wannan sani haka ba tare da ya yi wani karatu ba?"
16 Yesu ya amsa ya ce, "Koyarwata ba tawa ba ce, ta fito ne daga wurin wanda ya aiko ni. 17 Duk wanda ya zaɓi yin nufin Allah, zai gane ko koyarwata daga Allah ce, ko kuwa don kaina ne nake magana. 18 Mai magana don kansa, neman ɗaukakar kansa yake yi. Amma mai neman ɗaukakar wanda ya aiko shi, shi ne mai gaskiya, ba kuwa rashin gaskiya a gare shi.