4 suka kuma ce wa Yesu, "Malam, an kama wannan mace tana zina. 5 A cikin Doka Musa ya umarce mu, mu jajjefe irin waɗannan mata. To, me ka ce?" 6 Sun yi wannan tambaya ce don su sa masa tarko, don su sami hanyar zarge shi.
Amma Yesu ya sunkuya ya fara rubutu a ƙasa da yatsarsa. 7 Da suka ci gaba da yin masa tambayoyi, sai ya miƙe tsaye ya ce musu, "In da wani a cikinku da ba shi da zunubi, sai yă fara jifanta da dutse." 8 Sai ya sāke sunkuyawa ya kuma yi rubutu a ƙasa.
9 Da jin haka, waɗanda suka ji sai suka fara tashi daga wurin ɗaya-ɗaya, tun daga babbansu har ya zuwa ƙaraminsu, sai da aka bar Yesu kaɗai, tare da macen tsaye a wurin. 10 Sai Yesu ya miƙe tsaye ya tambaye ta ya ce, "Mace, ina suke? Ba wanda ya hukunta ki?"
11 Ta ce, "Ba kowa, ranka yă daɗe."
Sai Yesu ya ce, "Haka ni ma ban hukunta ki ba. Ki tafi, ki daina rayuwar zunubi."