Yesu ya warkar da mutumin da aka haifa makaho
1 Da Yesu yana tafiya, sai ya ga wani mutum wanda aka haifa makaho. 2 Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, "Rabbi, wane ne ya yi zunubi, mutumin ne, ko iyayensa, da ya sa aka haife shi makaho?"
3 Sai Yesu ya ce, "Ba don mutumin ko iyayensa sun yi zunubi ne ba, sai dai don a bayyana aikin Allah ne a rayuwarsa. 4 Muddin da sauran rana, dole mu yi aikin wanda ya aiko ni. Dare yana zuwa, sa’ad da ba wanda zai iya yin aiki. 5 Yayinda ina a cikin duniya, ni ne hasken duniya."
6 Bayan ya faɗi haka, sai ya tofa miyau a ƙasa, ya kwaɓa laka da miyau ɗin, ya kuma shafa a idanun mutumin. 7 Ya ce masa, "Je ka, ka wanke a Tafkin Silowam" (kalman nan tana nufin "Aikakke"). Saboda haka mutumin ya tafi ya wanke, ya kuma dawo gida yana gani.