10 "Ga shi, kamar yadda Ubangiji ya yi alkawari, ya bar ni da rai har na ƙara shekaru arba’in da biyar tun daga lokacin da ya gaya wa Musa wannan, a lokacin da Isra’ilawa suke yawo a cikin jeji. Ga ni nan yau shekaruna tamanin da biyar! 11 Ina nan da ƙarfina kamar yadda nake da ƙarfi a lokacin da Musa ya aike ni; zan iya fita zuwa yaƙi da ƙwazo yanzu kamar yadda nake zuwa a dā. 12 Yanzu sai ka ba ni wannan ƙasar da take kan tudu wadda Ubangiji ya yi alkawari zai ba ni a ranan nan. Kai ma ka ji a lokacin, yadda Anakawa suke a can, biranensu manya ne kuma sun kewaye su sosai, amma na sani Ubangiji zai taimake ni, zan kore su kamar yadda ya faɗa."
Publicidade