6 Sa’an nan matar ta tafi wajen mijinta ta faɗa masa cewa, "Wani mutumin Allah ya zo wurina. Ya yi kama da mala’ikan Allah, yana da bantsoro ƙwarai. Ban tambaye shi inda ya fito ba, kuma bai gaya mini sunansa ba. 7 Sai dai ya ce mini, ‘Za ki yi ciki, ki kuma haifi ɗa. To, fa, kada ki sha ruwan inabi ko abu mai sa maye kada kuma ki ci abin da yake marar tsarki, gama ɗan zai zama Banazare na Allah tun daga haihuwa har ranar mutuwarsa.’ "
8 Sai Manowa ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, "Ya Ubangiji, ina roƙonka, bari mutumin Allahn da ka aiko mana yă sāke zuwa don yă koya mana yadda za mu goyi yaron da za a haifa."