Pular para o conteúdo
Publicidade

Lucas 1

Waƙar Maryamu

46 Sai Maryamu ta ce,

"Raina yana ɗaukaka Ubangiji

47 ruhuna kuma yana farin ciki da Allah Mai Cetona,

48 gama ya lura da ƙasƙancin baiwarsa.

Daga yanzu nan gaba dukan zamanai za su ce da ni mai albarka,

49 gama Mai Iko Duka ya yi mini manyan abubuwa,

sunansa labudda Mai Tsarki ne.

50 Jinƙansa ya kai ga masu tsoronsa,

daga zamani zuwa zamani.

51 Ya aikata manyan ayyuka da hannunsa;

ya watsar da waɗanda suke masu girman kai a zurfin tunaninsu.

52 Ya saukar da masu mulki daga gadajen sarautarsu

amma ya ɗaukaka ƙasƙantattu.

53 Ya ƙosar da masu yunwa da kyawawan abubuwa

amma ya sallami mawadata hannu wofi.

54 Ya taimaki bawansa Isra’ila,

yana tunawa nuna jinƙai

55 ga Ibrahim da zuriyarsa har abada,

kamar yadda ya faɗa wa kakanninmu."

Veja também