59 A rana ta takwas, sai suka zo don a yi wa yaron kaciya, dā za su sa masa sunan mahaifinsa Zakariya ne, 60 amma mahaifiyar yaron ta ce, "A’a! Za a ce da shi Yohanna."
61 Sai suka ce mata, "Ba wani a cikin danginku mai wannan suna."
62 Sai suka yi alamu wa mahaifinsa, don su san sunan da zai su a kira yaron. 63 Ya yi alama a kawo masa allo, a gaban kowa sai ya rubuta, "Sunansa Yohanna." Dukan mutane kuwa suka yi mamaki.