Pular para o conteúdo
Publicidade

Lucas 1

Waƙar Zakariya

67 Mahaifinsa Zakariya ya cika da Ruhu Mai Tsarki sai ya yi annabci ya ce,

68 "Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila,

domin ya zo ya kuma fanshe mutanensa.

69 Ya mana ƙahon ceto

a gidan bawansa Dawuda

70 (yadda ya yi magana tun tuni ta wurin annabawansa masu tsarki),

71 cewa zai cece mu daga abokan gābanmu

daga kuma hannun dukan waɗanda suke ƙinmu

72 don nuna jinƙai ga kakanninmu,

kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki,

73 rantsuwar da ya yi wa mahaifinmu Ibrahim,

74 don kuɓutar da mu daga hannun abokan gābanmu,

kuma sa mu iya yin masa hidima babu tsoro,

75 cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakinmu.

76 "Kai kuma, ɗana, za a ce da kai annabin Maɗaukaki;

gama za ka sha gaban Ubangiji don ka shirya masa hanya,

77 don ka sanar da mutanensa ceto,

ta wurin gafarar zunubansu,

78 saboda jinƙai na Allahnmu mai ƙauna,

hasken nan na ceto zai ɓullo mana daga sama,

79 don haskaka a kan waɗanda suke zama cikin duhu,

da kuma cikin inuwar mutuwa,

don bi da ƙafafunmu a hanyar salama."

Veja também