Publicidade

Lucas 10

Misalin mutumin Samariya nagari

25 Wata rana, sai wani masanin dokoki ya miƙe tsaye don gwada Yesu. Ya tambaya ya ce, "Malam, me zan yi don in gāji rai madawwami?"

26 Yesu ya amsa ya ce, "Me aka rubuta a cikin Doka? Yaya kake karanta ta?"

27 Sai ya amsa ya ce, " Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka, da kuma dukan hankalinka; kuma, Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ "

28 Yesu ya ce, "Ka amsa daidai. Ka yi haka, kuma za ka rayu."

Veja também

Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-