29 Kada ku sa zuciyarku a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kada ku damu a kan su. 30 Gama duniya da ba tă san Allah ba, tana faman neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa, ya san kuna bukatarsu. 31 Amma ku nemi mulkinsa, za a kuwa ƙara muku waɗannan abubuwa.