4 "Ina dai gaya muku abokaina, kada ku ji tsoron masu kashe jiki, amma bayan haka, ba sauran abin da za su iya yi. 5 Amma zan nuna muku wanda za ku ji tsoronsa. Ku ji tsoron wanda, bayan da ya kashe jikin, yana da iko ya jefa ku cikin jahannama ta wuta. I, ina gaya muku, ku ji tsoronsa.
Publicidade
Publicidade