Misalai na ƙwayar mustad da na yisti
18 Sai Yesu ya yi tambaya ya ce, "Yaya mulkin Allah yake? Da me zan kwatanta shi? 19 Yana kama da ƙwayar mustad, wadda wani mutum ya ɗauka, kuma ya shuka a gonarsa. Ta yi girma, ta zama itace, kuma tsuntsayen sararin sama suka huta a rassansa."