Yesu a gidan Bafarisiye
1 Wata ranar Asabbaci, da Yesu ya shiga gidan wani sanannen Bafarisiye don cin abinci, sai mutane suka zuba masa ido da kyau. 2 A nan a gabansa kuwa akwai wani mutum mai ciwon kumburin ƙafa da hannu. 3 Sai Yesu ya tambayi masanan dokoki da Farisiyawa ya ce, "Daidai ne bisa ga doka, a yi warkarwa a ranar Asabbaci, ko babu?" 4 Amma ba su ce kome ba. Sai ya riƙe mutumin, ya warkar da shi, sa’an nan ya sallame shi.