Pular para o conteúdo
Publicidade

Luka 15:12-14,16-18,20

12 Ƙaramin ya ce wa mahaifinsu, ‘Baba, ba ni rabon gādona.’ Sai mahaifin ya raba musu dukiyarsa.

13 "Bayan ’yan kwanaki, sai ƙaramin ɗan ya tattara kayansa duk, ya tashi ya tafi wata ƙasa mai nisa. A can, ya ɓatar da dukiyarsa duka a rayuwar banza. 14 Bayan ya ɓatar da kome, sai ga muguwar yunwa a dukan ƙasar, har ya shiga rashi. 16 Ya yi marmarin cin dusan da aladun suke ci, amma ba wanda ya ba shi wani abu.

17 "Da hankalinsa ya dawo, sai ya ce, ‘Kai, bayin mahaifina guda nawa ne, da suke da abinci fiye da isashe, ni kuma ina nan, zan mutu don yunwa! 18 Zan tashi in koma wurin mahaifina, in ce masa, "Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi. 20 Sai ya tashi ya kama hanya ya koma wurin mahaifinsa.

"Amma tun yana nesa, mahaifinsa ya hange shi. Tausayi kuma ya kama shi, sai ya tashi ya ruga da gudu wurinsa, ya rungume shi, ya yi masa sumba.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.