Publicidade

Lucas 17

12 Da zai shiga wani ƙauye, sai maza goma da suke da kuturta suka sadu da shi. Suka tsaya da nesa, 13 suka yi kira da babbar murya, suka ce, "Yesu, Ubangiji, ka ji tausayinmu!"

14 Da ya gan su sai ya ce, "Ku je ku nuna kanku ga firistoci." Suna kan hanyar tafiya sai suka tsabtacce.

15 Da ɗayansu ya ga ya warke, sai ya koma, yana yabon Allah da babbar murya. 16 Ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, ya gode masa. Shi kuwa mutumin Samariya ne.

17 Yesu ya yi tambaya ya ce, "Ba duka goma ne aka tsabtacce ba? Ina sauran taran? 18 Ba wanda ya dawo don yabi Allah, sai dai wannan baƙon?" 19 Sai ya ce masa, "Tashi, ka yi tafiyarka, bangaskiyarka ta warkar da kai."

Veja também

Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-