Publicidade

Lucas 18

Misalin gwauruwa mai naciya

1 Yesu ya ba wa almajiransa wani misali, don koya musu yadda ya kamata su dinga yin addu’a kullum, ban da fasawa. 2 Ya ce, "A wani gari, an yi wani alƙali wanda ba ya tsoron Allah, bai kuma kula da mutane ba. 3 A garin nan kuma, akwai wata gwauruwa, wadda ta dinga zuwa wurin alƙalin nan, da roƙo cewa, Ka yi mini adalci tsakanina da maƙiyina.

4 "An daɗe yana ƙi, amma a ƙarshe ya ce cikin tunaninsa, Ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma kula da mutane ba, 5 amma don gwauruwan nan ta dame ni, zan tabbatar cewa ta sami adalci, domin kada gajiyar da ni, da yawan zuwanta.’ "

6 Sai Ubangiji ya ce, "Ku ji fa abin da alƙalin nan, marar gaskiya, ya ce. 7 Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke masa kuka, dare da rana adalci ba? Zai ci gaba da ƙin sauraronsu ne? 8 Ina gaya muku, zai tabbatar sun sami adalci, ban da ɓatan lokaci. Amma sa’ad da Ɗan Mutum ya dawo, zai sami bangaskiya a duniya ke nan?"

Veja também

Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-