Makaho mai bara ya sami ganin gari
35 Da Yesu ya yi kusa da Yeriko, akwai wani makaho da yake zaune a gefen hanya, yana bara. 36 Da ya ji taron suna wucewa, sai ya yi tambaya ko mene ne ke faruwa. 37 Suka ce masa, "Ai, Yesu Banazare ne ke wucewa."
38 Sai ya yi kira ya ce, "Yesu, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!"
39 Mutane da suke gaba suka kwaɓe shi, suka ce masa ya yi shiru. Amma sai ya ƙara ɗaga murya, yana cewa, "Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!"
40 Sai Yesu ya tsaya, ya ba da umarni a kawo mutumin wurinsa. Da ya zo kusa, Yesu ya tambaye shi ya ce, 41 "Me kake so in yi maka?"
Sai ya amsa ya ce, "Ubangiji, ina so in sami ganin gari."
42 Yesu ya ce masa, "Ka sami ganin garinka; bangaskiyarka ta warkar da kai." 43 Nan da nan, ya sami ganin garinsa, kuma ya bi Yesu, yana yabon Allah. Da dukan mutane suka ga wannan, sai su ma suka yabi Allah.