2 Akwai wani mutum a garin, mai suna Zakka. Shi shugaban masu karɓar haraji ne, mai arziki kuma. 3 Ya so yă ga ko wane ne Yesu, amma saboda taron, bai iya ba, domin shi gajere ne. 4 Saboda haka, ya yi gaba da gudu, kuma ya hau itacen sikamo, don yă gan shi, tun da Yesu zai bi wannan hanyar ne.
5 Da Yesu ya iso wurin, sai ya ɗaga ido sama, ya ce masa, "Zakka, ka yi maza ka sauka. Ni kam, dole in sauka a gidanka yau." 6 Sai ya sauka nan da nan, ya karɓe shi da murna.
7 Dukan mutane suka ga haka, kuma suka fara gunaguni, suka ce, "Ya je don yă zama baƙon ‘mai zunubi.’ "
8 Amma Zakka ya tashi a tsaye, ya ce wa Ubangiji, "Duba, Ubangiji! Nan take, rabin dukiyar da nake da shi, na ba wa matalauta. In kuma na taɓa cutan wani, a kan wani abu, zan mayar da shi ninki huɗu."