Pular para o conteúdo
Publicidade

Lucas 2

15 Da mala’ikun suka bar su, su suka koma sama, sai makiyayan suka ce wa juna, "Mu je Betlehem mu ga wannan abin da ya faru, wanda Ubangiji ya sanar mana."

16 Sai suka tafi da sauri, suka tarar da Maryamu da Yusuf, da kuma jaririn kwance a kwami. 17 Sa’ad da suka gan shi, sai suka baza maganar da aka gaya musu game da yaron, 18 duk kuwa waɗanda suka ji wannan, suka yi mamaki a kan abin da makiyayan suka faɗa.

Veja também