Yesu a haikali
41 Kowace shekara, iyayen Yesu sukan je Urushalima don Bikin Ƙetarewa. 42 Da Yesu ya cika shekaru goma sha biyu, sai suka tafi Bikin bisa ga al’ada. 43 Bayan Bikin, da iyayen suka kama hanya don su koma gida, sai Yesu, yaron nan, ya tsaya a Urushalima, ba da saninsu ba. 44 Su kuwa sun ɗauka yana tare da su, saboda haka, suka yi ta tafiya har na yini guda. Sa’an nan suka fara nemansa cikin ’yan’uwansu da abokansu. 45 Da ba su gan shi ba, sai suka koma Urushalima nemansa. 46 Bayan kwana uku, sai suka same shi a filin haikali zaune a tsakiyar malamai, yana sauraronsu yana kuma yi musu tambayoyi. 47 Dukan waɗanda suka ji shi, suka yi mamakin fahimtarsa, da amsoshinsa. 48 Da iyayensa suka gan shi sai suka yi mamaki. Mahaifiyarsa ta ce masa, "Ɗana, don me ka yi mana haka? Ni da mahaifinka duk mun damu muna nemanka."
49 Sai ya ce, "Don me kuke nemana? Ba ku san cewa, dole in kasance a gidan Ubana ba?" 50 Amma ba su fahimci abin da yake faɗin musu ba.
51 Sai ya koma Nazaret tare da su, yana yi musu biyayya. Mahaifiyarsa kuma ta riƙe dukan waɗannan abubuwa a zuciyarta. 52 Yesu kuwa ya yi girma, ya kuma ƙaru cikin hikima, ya kuma sami tagomashi a wurin Allah da mutane.