Ba wa waɗansu laifi
37 "Kada ku ɗora wa wani, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yanke wa wani hukunci, ku ma ba za a yanke muku ba. Ku gafarta, ku ma za a gafarta muku. 38 Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har yă yi tozo, yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna da shi, da shi za a auna muku."