Publicidade

Lucas 6

Itace da ya’yansa

43 "Ba itace mai kyau da yake ba da munanan ya’ya. Mummunan itace kuma ba ya ba da ya’ya masu kyau. 44 Kowane itace da irin ya’yansa ne ake saninsa. Mutane ba sa tsinke ya’yan ɓaure daga ƙaya, ko kuwa ya’yan inabi daga sarƙaƙƙiya. 45 Mutumin nagari yakan nuna abubuwa nagari daga cikin nagarta da yake a ɓoye a zuciyarsa, mugun mutum kuwa yakan nuna mugayen abubuwa daga muguntar da take a ɓoye a zuciyarsa. Gama baki yakan faɗa abin da ya cika zuciya ne."

Veja também

Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-