6 A wata ranar Asabbaci kuma, Yesu ya shiga majami’a yana koyarwa. To, a nan kuwa akwai wani mutumin da hannun damansa ya shanye. 7 Farisiyawa da malaman dokoki suka zuba wa Yesu ido, su ga ko zai warkar a ranar Asabbaci, don su sami dalilin zarginsa. 8 Amma Yesu ya san abin da suke tunani. Sai ya ce wa mutumin mai shanyayyen hannun, "Tashi ka tsaya a gaban kowa." Sai ya tashi ya tsaya.
9 Yesu ya ce musu, "Ina tambayarku, me ya kamata a yi bisa ga doka, a ranar Asabbaci, a aikata alheri ko a aikata mugunta, a ceci rai, ko a hallaka shi?"
10 Sai ya kalle su duka, sa’an nan ya ce wa mutumin, "Miƙo hannunka." Sai ya miƙe, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye.