Yarinya da ta mutu da mace marar lafiya
40 Da Yesu ya koma, taron suka marabce shi, don dā ma duk suna jiransa. 41 Sai wani mutum mai suna Yayirus, wani mai mulkin majami’a, ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, yana roƙonsa ya zo gidansa, 42 domin diyarsa ɗaya tak, wadda ta kai shekara goma sha biyu, tana bakin mutuwa. Da Yesu yake kan hanyarsa, taron mutane masu yawa suka yi ta matsa shi a kowane gefe. 43 A wurin kuwa, akwai wata mace wadda tana da ciwon zubar da jini, har na shekara goma sha biyu, amma babu wanda ya iya warkar da ita. 44 Sai ta zo ta bayansa, ta taɓa bakin rigarsa. Nan da nan, zubar da jininta ya tsaya.
45 Yesu ya yi tambaya, "Wa ya taɓa ni?"
Bayan kowa ya yi musu, sai Bitrus ya ce, "Ubangiji, ai, mutane da yawa suna matsinka ta kowane gefe."
46 Amma Yesu ya ce, "Wani ya taɓa ni, na san cewa iko ya fita daga wurina."
47 Sai macen, da ta ga ba halin ɓoyewa, sai ta fita, jikinta na rawa, ta fāɗi a gabansa. A gaban dukan mutanen, ta faɗi dalilin da ya sa ta taɓa shi, da yadda ta warke nan take. 48 Sai Yesu ya ce mata, "Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya."
49 Yayinda Yesu na cikin magana har yanzu, sai ga wani daga gidan Yayirus, mai mulkin majami’ar ya ce, "Kada ka ƙara damun malam, diyarka ta rasu."
50 Da Yesu ya ji wannan, sai ya ce wa Yayirus, "Kada ka ji tsoro, ka gaskata, za a kuma warkar da ita."
51 Da ya iso gidan Yayirus, sai ya hana kowa yă bi shi cikin ɗakin, sai dai Bitrus, da Yohanna, da Yaƙub, da kuma mahaifin da mahaifiyar. 52 Ana cikin haka, dukan mutanen kuma sai kuka da makoki suke ta yi, domin yarinyar. Sai Yesu ya ce, "Ka daina yin kuka, ba tă mutu ba, tana barci ne."
53 Sai suka yi masa dariya, da yake sun san cewa, ta mutu. 54 Amma Yesu ya kama ta a hannu ya ce, "Diyata, tashi." 55 Ruhunta ya dawo, kuma ta tashi, nan take. Yesu ya ce musu, su ba ta wani abu tă ci. 56 Iyayenta suka yi mamaki, amma ya ba su umarni kada su faɗa wa kowa abin da ya faru.