Pular para o conteúdo
Publicidade

Lucas 8

49 Yayinda Yesu na cikin magana har yanzu, sai ga wani daga gidan Yayirus, mai mulkin majami’ar ya ce, "Kada ka ƙara damun malam, diyarka ta rasu."

50 Da Yesu ya ji wannan, sai ya ce wa Yayirus, "Kada ka ji tsoro, ka gaskata, za a kuma warkar da ita."

51 Da ya iso gidan Yayirus, sai ya hana kowa bi shi cikin ɗakin, sai dai Bitrus, da Yohanna, da Yaƙub, da kuma mahaifin da mahaifiyar. 52 Ana cikin haka, dukan mutanen kuma sai kuka da makoki suke ta yi, domin yarinyar. Sai Yesu ya ce, "Ka daina yin kuka, ba mutu ba, tana barci ne."

53 Sai suka yi masa dariya, da yake sun san cewa, ta mutu. 54 Amma Yesu ya kama ta a hannu ya ce, "Diyata, tashi." 55 Ruhunta ya dawo, kuma ta tashi, nan take. Yesu ya ce musu, su ba ta wani abu ci. 56 Iyayenta suka yi mamaki, amma ya ba su umarni kada su faɗa wa kowa abin da ya faru.

Veja também