Pular para o conteúdo
Publicidade

Lucas 9

12 Da rana ta kusa fāɗuwa, sai Sha Biyun suka zo wurinsa, suka ce, "Ka sallami taron domin su shiga ƙauyuka na kewaye, su nemi abin da za su ci, da wurin kwana, don inda muke, ba kowa."

13 Yesu ya ce, "Ku, ku ba su wani abu su ci."

Sai suka ce masa, "Muna da burodi biyar da kifi biyu kaɗai. Sai dai, in mun je mu sayi abinci domin dukan wannan taron." 14 Maza kaɗai sun kai kusan dubu biyar.

Amma ya ce wa almajiransa, "Ku sa su su zauna a ƙungiya hamsin-hamsin." 15 Haka almajiran suka yi, kowa kuwa ya zauna. 16 Sai Yesu ya ɗauki burodin biyar da kifin biyun, ya ɗaga kansa sama, ya yi godiya, ya kuma kakkarya su. Ya ba wa almajiransa, domin su rarraba wa mutanen. 17 Duka kuwa suka ci suka ƙoshi. Almajiran suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna goma sha biyu.

Veja também