Pular para o conteúdo
Publicidade

Lucas 9

Wahalar bin Yesu

57 Suna kan tafiya a hanya, sai wani mutum ya ce masa, "Zan bi ka, duk inda za ka."

58 Yesu ya ce, "Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama suna da sheƙuna, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa."

59 Ya kuma ce wa wani mutum, "Ka bi ni."

Amma mutumin ya amsa ya ce, "Ubangiji, bari in je in binne mahaifina tukuna."

60 Yesu ya ce masa, "Ka bar matattu su binne matattunsu, amma kai, ka je ka yi shelar mulkin Allah."

61 Har wa yau, wani ya ce, "Zan bi ka, Ubangiji, amma ka bar ni in je in yi bankwana da iyalina tukuna."

62 Yesu ya amsa ya ce, "Babu wani da yakan sa hannunsa a garman shanu, sa’an nan ya waiwaya baya, da ya isa ya shiga hidima a cikin mulkin Allah ba."

Veja também