23 Nan take, sai wani mutum mai mugun ruhu a majami’arsu, ya ɗaga murya ya ce, 24 "Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, Mai Tsarki nan na Allah!"
25 Yesu ya tsawata masa ya ce, "Yi shiru! Fita daga cikinsa!" 26 Sai mugun ruhun ya jijjiga mutumin da ƙarfi, ya fita daga jikinsa da ihu.