Pular para o conteúdo
Publicidade

Marcos 11

Shiga mai nasara

1 Sa’ad da suka yi kusa da Urushalima, suka zo Betfaji da Betani wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki biyu daga cikin almajiransa, 2 ya ce musu, "Ku je ƙauyen da yake gaba da ku, da shigarku, za ku tarar da wani ɗan jaki a daure a can, wanda ba wanda ya taɓa hawa. Ku kunce shi ku kawo nan. 3 In wani ya tambaye ku, Don me kuke yin haka?Ku gaya masa cewa, Ubangiji yana bukatarsa, zai kuma dawo da shi ba da jimawa ba.’ "

4 Suka tafi, suka kuwa tarar da wani ɗan jaki a waje, a titi, daure a ƙofar gida. Suna cikin kunce shi ke nan, 5 sai waɗansu mutane da suke tsattsaye a wurin suka ce musu, "Me kuke yi da kuke kunce ɗan jakin nan?" 6 Suka amsa kamar yadda Yesu ya ce su yi. Mutanen kuwa suka ƙyale su. 7 Da suka kawo shi wajen Yesu, sai suka shimfiɗa rigunarsu a bayansa. Yesu kuwa ya hau ya zauna bisansa. 8 Mutane da yawa suka shimfiɗa rigunarsu a kan hanya, waɗansu kuma suka baza rassan itatuwan da suka sara daga gonaki. 9 Waɗanda suka yi gaba, da kuma waɗanda suke biye, duk suka ɗaga murya, suna cewa,

"Hosanna!11.9 Wani faɗi ne na Ibraniyanci mai ma’ana "Ceto!" Wanda ya zama kalmar yabo; haka ma a aya 10"

"Mai albarka ne wanda yake zuwa a cikin sunan Ubangiji!"11.9 Zab 118.25; Zab 118.26

10 "Mai albarka ne mulkin nan mai zuwa na mahaifinmu Dawuda!"

"Hosanna a can cikin samaniya!"

11 Yesu ya shiga Urushalima ya kuma tafi filin haikali. Ya dudduba kome duka, amma da yake yamma ta yi, sai ya tafi Betani tare da Sha Biyun.

Veja também