Pular para o conteúdo
Publicidade

Marcos 11

Itacen ɓaure da ya yanƙwane

20 Da safe, da suke wucewa, sai suka ga itacen ɓauren nan ya yanƙwane tun daga saiwarsa. 21 Bitrus ya tuna, sai ya ce wa Yesu, "Rabbi, duba! Itacen ɓauren nan da ka la’anta, ya yanƙwane!"

22 Yesu ya amsa ya ce, "Ku gaskata da Allah. 23 Gaskiya nake gaya muku, in wani ya ce wa dutsen nan, Je ka, ka fāɗa cikin teku,bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata cewa, abin da ya faɗa zai faru, haka kuwa za a yi masa. 24 Saboda haka, ina faɗa muku, duk abin da kuka roƙa cikin addu’a, ku gaskata kun riga kun karɓa, zai kuwa zama naku. 25 A duk lokacin da kuke tsaye cikin addu’a, in kuna riƙe da wani mutum a zuciyarku, ku gafarta masa, domin Ubanku da yake sama shi ma gafarta muku zunubanku."11.25 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da zunubai. 26 Amma idan ba kwa yafewa, Ubanku ma da yake sama, ba zai yafe muku zunubanku ba.

Veja também