Pular para o conteúdo
Publicidade

Marcos 2

3 Waɗansu mutum huɗu suka zo wajensa ɗauke da wani shanyayye. 4 Da ba su iya kai shi wurin Yesu ba, saboda taron, sai suka buɗe rufin gidan saman, bisa daidai inda Yesu yake. Bayan da suka huda rami, sai suka saukar da shanyayyen, kwance a kan tabarmarsa. 5 Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, "Saurayi, an gafarta zunubanka."

6 To, waɗansu malaman dokoki da suke zaune a wurin, suka yi tunani a zuciyarsu, suna cewa, 7 "Me ya sa mutumin nan yake magana haka? Yana saɓo! Wane ne zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?"

8 Nan da nan, Yesu ya gane a ruhunsa abin da suke tunani a zuciyarsu, sai ya ce musu, "Me ya sa kuke tunanin waɗannan abubuwa? 9 Wanne ya fi sauƙi, a ce wa shanyayyen, An gafarta zunubanka,ko a ce, Tashi, ɗauki tabarmarka ka yi tafiya? 10 Amma don ku san cewa, Ɗan Mutum yana da iko a duniya gafarta zunubai." Sai ya ce wa shanyayyen, 11 "Ina ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka, ka tafi gida." 12 Sai ya tashi, ya ɗauki tabarmarsa, ya yi tafiyarsa a gabansu duka. Wannan ya ba wa kowa mamaki, suka kuma ɗaukaka Allah suna cewa, "Ba mu taɓa ganin abu haka ba!"

Veja também