Pular para o conteúdo
Publicidade

Marcos 3

Mahaifiyar Yesu da yan’uwansa

31 Sai mahaifiyar Yesu tare da yan’uwansa suka iso. Suna tsaye a waje, sai suka aiki wani ciki kira shi. 32 Taron yana zaune kewaye da shi, sai suka ce masa, "Mahaifiyarka da yan’uwanka suna waje, suna nemanka."

33 Ya yi tambaya ya ce, "Su wane ne mahaifiyata, da yan’uwana?"

34 Sai ya dubi waɗanda suke zaune kewaye da shi ya ce, "Ga mahaifiyata da yan’uwana! 35 Duk wanda yake aikata nufin Allah, shi ne ɗan’uwana, da yar’uwata, da kuma mahaifiyata."

Veja também