Pular para o conteúdo
Publicidade

Marcos 4

37 Sai babban hadari mai iska ya tashi, raƙuman ruwa suna ta bugun jirgin ruwan, har jirgin ruwan ya kusa cika da ruwa. 38 Yesu kuwa yana can baya, yana barci a kan katifa. Sai almajiran suka tashe shi suka ce masa, "Malam, ba ka kula ba ko mu nutse?"

39 Sai ya farka ya tsawata wa iskar, ya ce wa raƙuman ruwan, "Shiru! Ku natsu!" Sai iskar ta kwanta, kome kuma ya yi tsit.

40 Sai ya ce wa almajiransa, "Don me kuke tsoro haka? Har yanzu ba ku da bangaskiya ne?"

41 Suka tsorata, suka ce wa juna, "Wane ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa ma suna masa biyayya!"

Veja também