25 A can kuwa akwai wata mace, wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini. 26 Ta kuma sha wahala ƙwarai a hannun likitoci da yawa, har ta kashe duk abin da take da shi, amma maimakon samun sauƙi, sai ciwon ya ƙara muni. 27 Da ta ji labarin Yesu, sai ta zo ta bayansa, a cikin taron, ta taɓa rigarsa, 28 domin ta yi tunani cewa, "Ko da rigunarsa ma na taɓa, zan warke." 29 Nan da take, zub da jininta ya tsaya, sai ta ji a jikinta ta rabu da shan wahalarta.