22 Sa’ad da diyar Hiridiyas ta shigo, ta kuma yi rawa, sai ta gamshi Hiridus tare da baƙinsa.
Sai Sarkin ya ce wa yarinyar, "Ki tambaye ni kome da kike so, ni kuwa zan ba ki." 23 Ya yi mata alkawari da rantsuwa cewa, "Duk abin da kika roƙa, zan ba ki, ko da rabin mulkina ne."
24 Sai ta fita ta ce wa mahaifiyarta, "Me zan roƙa?"
Ta ce, "Kan Yohanna Mai Baftisma."
25 Nan da nan, sai yarinyar ta yi hanzari zuwa wajen sarki da roƙon, "Ina so ka ba ni kan Yohanna Mai Baftisma a cikin tasa, yanzu-yanzu nan."
26 Sai sarki ya yi baƙin ciki ƙwarai, amma saboda rantsuwar da kuma baƙinsa, bai so yă hana ta ba. 27 Nan take, sai ya aiki mai aiwatar da kisa da umarni ya kawo kan Yohanna. Mutumin ya je ya yanke kan Yohanna a kurkuku. 28 Ya kuma kawo kan a tasa ya ba yarinyar. Ita kuma ta ba wa mahaifiyarta.