Pular para o conteúdo
Publicidade

Marcos 7

Bangaskiyar Baheleniya

24 Sai Yesu ya bar wurin, ya kuma tafi wajajen Taya. Ya shiga wani gida, bai kuwa so kowa sani ba. Duk da haka, bai iya ɓoye kasancewarsa ba. 25 Da jin labarinsa, sai wata mace wadda ƙaramar diyarta tana da mugun ruhu, ta zo ta durƙusa a gabansa. 26 Macen kuwa mutuniyar Hellenawa ce, an haife ta a Funisiya a Suriya. Ta roƙi Yesu fitar da aljani da yake jikin diyarta.

27 Yesu ya ce mata, "Da farko, bari ya’ya su ci su ƙoshi tukuna, gama ba daidai ba ne, a ɗauki burodin yara a jefa wa karnukansu."

28 Ta amsa, ta ce, "I, Ubangiji, ko karnuka ma da suke ƙarƙashin tebur, sukan ci burbuɗin da suke fāɗuwa daga abincin yara."

29 Sai ya ce mata, "Saboda irin wannan amsa, ki tafi, aljanin ya rabu da diyarki."

30 Ta tafi gida, ta tarar da diyarta kwance a gado, aljanin kuwa ya fita.

Veja também